xxx_one_+_love
KALAMAI MASU SANYAYA ZUCIYA Gari ya waye ALFIJIR yaketo ,tsananin sanyin safiya,iska na kadawa . Alokacinda xakaru ke cara ,alokacinda yabonki tsananin kaunarki ke kara kutsawa cikin zuciyata Wani lokacin sai inkasa zaune inkasa tsaye ke kawai nake tunawa ,ya'abar alfaharina, Da sonki nake kwana da sonki nake tashi Aduk bugun numfashina kece halittar danake tunawa ,samunki akusa dani shine burin zuciya da sauran sassan jikina . Nafison ace na sameki dan gusarda duk wani bakin ciki dake cikin zuciyata Kece sanyin zuciyata da kwanciyar hankalina.
Comments