BEEN JFR TAGWAYE (GYARAN FUSKA) amare da dama suna fama da matsalar kurajen fuska musamman farar mace Wanda sune sukafi fuskantar wannan matsalar Zanyi bayanin hanyoyi goma Wanda amarya zatabi don magance matsalar kurajen fuska (1) Da farko ana so awa biyu ko uku kafin ki kwanta barci sai ki shafa man goge baki a fuskarki, musamman wuraren da kurajen pimples suke da yawa. Ba kowane irin man goge baki za ki shafa ba, ana so ki shafa farin man goge baki ne. Idan kin ga dama za ki iya wanke fuskarki idan man goge bakin da kika shafa ya kai minti 30, idan kin ga dama kuma za ki iya kwantawa da shi har zuwa wayewar gari. Za ki rika maimata hakan har zuwa wadansu kwanaki, idan kin yi hakan za ki ga canji a fuskarki. (2) Ki kasance mai yawan shan ruwa.yawaita shan ruwa ba wai zai sanya miki laushin fata ba ne kawai, a’a, zai taimaka miki wajen yaki da kurajen pimples din da suke fuskarki. Haka yana da kyau ki guji yawan cin abincin gwangwani, kasancewar suna dauke da wasu sinadarai da z...
Comments